Dole Sai Buhari Ya duba Bukatar Masu Neman Kafa Biafra – Majalisar Sarakunan IgboMajalisar sarakunan jihohin Kudu maso Gabas wato ‘yan kabilar Igbo ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan dole ya duba bukatun kungiyoyin da ke fafitikar kafa kasar Igbo zalla ta Biyafara.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da suka kai wa Shugaba Buhari a fadarsa a karkashin jagorancin Shugaba majalisar, Mai Martaba Dr. Eberechi N. Dick inda suka nuna wa Shugaban kasan bukatar yin zaman sulhu da kungiyoyin don samun zaman lafiya a yanki.
Da yake mayar da martani Shugaba Buhari ya nemi masu Fafitkar kafa kasar Biyafaran kan su sake tunani inda ya nuna cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani yunkurin da zai yi barazana ga zaman Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa ba.

You may also like