Dole Sai ‘Yan Najeriya Sun Canza Halinsu Za’a Samu Sauqin Rayuwa – Maitama Sule


Tsohon jakadan Nijeriya a majalisar dinkin duniya, Dakta Yusuf Maitama Sule (Danmasanin Kano) ya baiwa ‘yan Nijeriya shawara cewa idan har ana so kasar nan ta gyaru, sai kowa ya gyara halinsa.
Maitama Sule ya bayyana hakan ne a gidan sa da ke Kano lokacin da  Sanata Shehu Sani ya kai masa ziyara. 
Maitama Sule yace Nijeriya na bukatar Shugabannin kirki a wannan lokaci, saidai Dattijon ya ce ba za a taba samun irin wadannan Shugabannin na kwarai ba har sai an samu wani juyin-juya-hali a kasar.
Maitama Sule ya ce ba juyin-juya-hali na tada fitina yake nufi ba, kamar wanda Tse-Tung ya kawo a Kasar China mutane miliyan 70 suka rasa rayuwar su, ko wanda Gandhi ya yi a India. Yace abin da yake nufi, kowa ya sauya halinsa.
Maitama Sule, mai shekaru kusan 87 a duniya ya ce  za a samu wannan sauyin ne idan ‘yan Nijeriya sun canza halin su.
 Maitama Sule yace kaf Afrika ana bukatar Shugabannin nagari, amma ba za a taba samun Shugabannin ba sai mabiya sun canza halayen su, sun koma na kirki. Ya kara da bayyana cewan Shugabanni na kirki ake bukata ba Shugabannin sace kudin al’umma ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like