Kotun koli a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara dake Kaduna wacce ta amince da shari’ar tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema kan zarginsa da ake na almundahanar wasu kuɗaɗe kimanin biliyan ₦11.
Shema wanda shine gwamnan jihar Katsina tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015 na fuskantar shari’a tare da wasu mutane uku da suka haɗa da Sani Makana, Lawal Safana da kuma Ibrahim Dankaba.
Da yake sanar da hukuncin amadadin sauran alkalan mai shari’a Sadi Bage yace kundin tsarin mulki ya bawa hukumar EFCC ikon tuhumar mutumin da ake zargi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati a matakin jiha ko kuma tarayya.
EFCC ta gurfanar da Shema tare da wasu mutane uku a gaban mai shari’a Maikaita Bako na babbar kotun jihar kan zargin laifin zambatar jihar lokacin da yake gwamna na tsawon shekaru 8.
Tun da fari mutanen da ake kara sun ƙalubalanci hurumin kotun kan sauraron shari’ar inda suka yi ikirarin cewa EFCC bata da ikon gurfanar dasu gaban kotun.