Donald Trump: Obama babban dan ta’adda ne


 

Dantakarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republicans a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamban 2016 Donald Trump ya zargi shugaba Obama da kafa kungiyar ta’adda ta Daesh.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito cewa, Trump ya yi jawabi ga magoya bayansa a Florida inda sau uku ya ambaci Obama a matsayin wanda ya kafa kungiyar ta’adda ta Daesh.

A baya ma Trump ya zargi abokiyar takararsa Hillary Clinton a matsayin wadda ta kafa kungiyar ta Daesh.

Donald trump ya ce, manufofin Obama a Gabas ta Tsakiya ne suka sanya kungiyar ta Daesh karfafa da ma kafata tun asali.

Babu wata sanarwa da fadar White House ta yi game da zargin na Donald Trump.

You may also like