Donald Trump ya tsalake rijiya da baya


 

 

A yayin da yake jawabi a gaban mutanen yankin Nevada, sai jami’an leken asirin kasar Amurka suka yi kadaran-kadahan domin nesanta shi daga bainar jama’a ba tare da shirya ba.

Wannan lamarin da ya afku a daidai lokacin da ya kawo gaban goshin game da zaben shugaban kasar Amurka.

Jami’an tsaron sun kai wa Trump dauki dan tabbatar da tsaronsa a yayin da yake jawabi a gaban gungun mutanen.

Bayan sun kwantar da hankali kowa da kuma yin sintiri tsakiyar jama’a,sai Donald Trump ya sake bayyana a gaban magoya bayansa domin cigaba da jawabinsa inda ya ce : “Bamu taba furucin cewa wannan aiki na da sauki ba.Amma kuma ba zamu taba ja da baya ba.Ina mika godiyata ta musamman ga jami’an leken asiri”.

Kawo yanzu an kasa sanin takamaimen abin da ya faru a falon taron siyasar ,amma mutanen tawagar farko na wannan taron sun sanar da cewa an ga wani mutum dauke bindiga a tsakiyar jama’a.

You may also like