Hukumar DSS tayi namijin kokari bayan da ta damke wani Dan Boko Haram da ke shirin kai hari a cikin Garin Kaduna. Dan Boko Haram din dai ya tsero ne daga Jihar Yobe da niyyar tada kayar-baya a Garin na Kaduna.
Jami’an Tsaro na DSS dai sun yi nasarar kama wannan Dan Boko Haram kafin yayi ta’asa. Jami’in Hukumar Tony Opuiyo yace sun kama wani Dan Boko Haram mai suna Alkassim Salisu wanda ya shirya kai hari a cikin Kaduna.
‘Yan Boko Haram da dama sun tsero daga Yankin Arewa maso Gabashin Kasar bayan da Sojojin suka fatattako su. Maimakon wannan ya nemi zama lafiya, sai ya ma kuma fara shirin yadda zai kawo wani sabon rikici.
Hukumar DSS din suna cigaba da damke ‘Yan Boko Haram da sauran masu laifi a cikin Kasar. Hukumar tace tayi nasarar damke masu laifuffuka da dama a cikin Kasar; daga masu garkuwa da mutane zuwa ‘Yan ta’adda a garin Fatakwal, Taraba, Kogi, Legas, Kano, dsr.