DSS ta tabbatar da shirin wasu na kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a Najeriya



Ofishin DSS

Asalin hoton, DSS/Facebook

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta shaida wasu jiga-jigai a wata maƙarƙashiya ake kitsawa don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar.

Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wanda wasu ke izawa ba kawai abu ne da ya saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kaucewa.

Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokraɗiyya da kuma zaman lafiyar al’ummar ƙasar.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin za a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like