Dubai ta soke harajin barasa domin jan hankalin baki



Wani mai sayar da barasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai mutum yana da lasisi na musamman zai sayi barasa a Dubai

Hukumomin Dubai sun soke harajin da ake biya na kashi 30 cikin dari na sayen barasa a wani yunkuri da ake gani na kokarin zawarcin ‘yan yawon bude idanu ne.

Haka kuma jama’a za su daina biyan kudin harajin da suke bayarwa na ka’ida na samun izinin shan giyar a gida, wanda sai sun yi haka ne suke da damar sha ba tare da cewa sun keta doka ba.

A baya-bayan nan Dubai na ta sassauta dokokinta inda take bayar da damar sayar da barasa a fili kuma a rana tsaka hatta a cikin watan azumi na Ramadan, tare kuma da amincewa da kai barasar gidaje ga mabukata a lokacin annobar Korona.

Ana ganin duka wadannan matakan da hukumomin ke dauka wani kokari ne na jan ‘yan kasashen waje birnin domin gogayyar da suke fuskanta daga makwabtan kasashe.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like