Ma’aikatar dake kula da ‘yan gudun hijra ta kasar Iraki ta sanar da cewa daga Lokacin da aka fara kai farmakin ‘yanto garin Mosil daga hanun ‘yan ta’addar IS, duban Irakiyawa ne suke gudu daga hanun ‘yan ta’addar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alkhamis, Ma’aikatar dake kula da ‘yan gudun hijra na kasar Iraki ta ce daga Lokacin da aka fara kai farmakin ‘yanto garin Mosil daga hanun ‘yan ta’addar IS, irakiyawa dubu 11 da 735 ne suka yi hijra daga yankunan su da ya kasance kalkashin ikon ‘yan ta’addar IS.
A nasa bangare, Sfeto janar na ‘yan sandar tsakiyar kasar Iraki Ja’afar Albattat ya sanar da cewa Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar tsarkake kauyuka 59 dake kalkashin ikon ‘yan ta’addar IS a kudancin garin Mosil, baya ga haka Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’addar na IS sun zartar da hukunci kisa kan Mutane da dama mafi yawa daga ciki tsofin ‘yan sanda da sojoji ne, sannan kuma a yau din nan mayakan kungiyar ta IS sun fitar da marassa lafiya daga cikin asibitocin garin Mosil domin a kula da na su marassa lafiyar.
A bangare guda Janar Joseph Votel kwamandan Sojojin Amurka dake tsakiyar kasar Iraki ya sanar da cewa daga Lokacin da aka fara kai farmakin ‘yanto garin Mosil an hallaka ‘yan ta’addar IS tsakanin 800 zuwa 900.
A ranar 17 ga watan Oktoba ne aka fara kai farmaki na tsarkake garin Mosil daga hanun ‘yan ta’addar IS daga suka mamaye shi tun a watan yunin 2014.