Dubu 56,000 Ya Yi Kadan a Matsayin Mafi Karancin Albashi – Kungiyar Kwadago 



Kungiyar Kwadago ta gabatar da wani sabon tsarin albashi mafi karanci ga kwamitin Shugaban kasa na daidaita albashin ma’aikatan gwamnati.

Mukaddashin Shugaban Kwadago na kasa, Kwamred Kiri Mohammed ya ce, tsarin da ake hasashe na Naira 56,000 a matsayin mafi karancin albashi da za a rika biyan kowane ma’aikaci a Nijeriya ya yi kadan idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki a yanzu.

You may also like