Duk Ɗan Majalisar Da Yayi Yunƙurin Tsige Buhari, A Bakacin Kujerar Sa – Sen Kwankwaso



Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yace duk dan majalisa da yake gani wuyansa ya isa yanka ya yi kuskuren kawo kudirin tsige shugaba Buhari, to zai tabbatar da cewa ya debo wutar gasa kansa.

Kwankwaso yace “muna da labarin akwai wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai wasu ‘yan siyasa dake majalisa masu shirin kawo kudirin tsige shugaban kasa, to ina mai tabbatar masu da cewar kafin su tsige shugaban kasa to mune za mu yi maganinsu. Kuma za su gane kurensu.

Kwankwaso ya kara da cewa “ba za mu bar wasu tsiraru gurbatattu su tuge mana bishiyar mu ba, wacce muka dasa da hannun mu, kuma muna mata bayi harsai ta haihu kuma muna kyautata zaton duk dan Nijeriya sai ya ci ‘ya’yan wannan bishiyar”.

Sanata Kwankwaso ya shaida hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a fadar shugaban kasa a gaban gungun ‘yan jaridu bayan ganawar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan tsaron, ya kara da cewar har yanzu yana kyautata zaton shugaban kasa Buhari zai fitar da kasar daga halin da jam’iyyar PDP ta jefa ta. Tsohon gwamnan ya kuma roki ‘yan Nijeriya musamman ‘yan jam’iyyar su ta APC  mai mulki da su cigaba da marawa shugaban kasar baya da jam’iyayr APC don ganin sun yi nasara. Kana Kwankwaso ya roki ‘yan kasar da su ci gaba da addu’o’in samun cikekken lafiya ga shugaban kasar don ganin ya yi nasara.

You may also like