Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya ja hankalin masu rike da sarautun gargajiya kan dukan matansu, a inda ya ce duk mai rawanin da aka samu da laifin dukan matarsa to a bakin rawaninsa.
Muhammdu Sunusi ya kara da cewa a tsarin sarautar Kano duk mai sarauta walau dai hakimi ko dagaci ko kuma mai unguwa har ma limami da aka kai fada yana dukan matarsa to zai ajiye rawaninsa.