Duk Mai Son Ganin Bala’i Da Idonso To Ya Taba Manzon Allah ( S. A. W) – KABIRU GOMBE“Duk wanda ya ke Najeriya ya ji maganganun da wani Malamin Bidi’a ya yi akan Ahlus Sunnah. Ba akan Ahlus Sunnah kawai ba har da shugaban Ahlus Sunnah Abdullahi Bala Lau.

 A lokacin da mai zagi yayi zagi. Mai makirci yayi makirci. Mai sharri yayi sharri sai shugaba ya fito ya ce, Lura da shekarun ka da kuma Lura da wasu Mutane da ke tare da kai ba zan maimaita abinda ka fada a kaina ba. Wannan ita ce akida ta Ahlus Sunnah. Ahlus Sunnah idan ka zage shi ba ramawa zai yi ba. In kayi masa karya ba ramawa zai yi ba. In kayi masa sharri ba ramawa zai yi ba. Saboda me? Saboda ba da kai aka ce yayi koyi ba. 

Shi an ce yayi koyi ne da wa? Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Shi kuma Annabin mu baya karya. Shi kuma Annabin mu baya sharri. Shi kuma Annabin mu baya makirci. Shi ya sa duk wadanda suka zagi Annabi amma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam bai rama ba. Ya fi kowa gaskiya suka ce makaryaci ya ne. Ya fi kowa amana suka ce maha’inci ne. Ya fi kowa IMANI suka ce Boka ne. 

Ya fi kowa hankali a duniya suka ce mahaukaci ne. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam bai taba yin ramuwar gayya don an zage shi ko an soke shi ba. Idan ka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ransa ya baci, hankalin sa ya tashi, idanuwansa sun yi ja to Allah a taba. An keta dokar Ubangiji. Wannan ne dalilin da ya sa Ahlus Sunnah a duniya idan ka ga suna zafin Kai suna tayar da jijiyar wuya to an taba Allah ko an taba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. 

Yana daga alamar da ake gane dan Bidi’a daukar zafi idan aka taba Malamin sa ko an taba Shehun sa. Mu idan ka fito ka zagi Sheikh Mahmud Gumi ka ce Gumi gungumen wutar Jahannama. Sai mu ce wannan matsalar mai sauki ce, kai da Gumi Allah zai yi musu hisabi ranar tashin Alkiyama. Idan kana son ganin an yi Bala’i har ma ka ga Bala’i da idonka to taba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam”.

Sheikh Kabiru Gombe a yayin gudanar da babban Wa’azin Kasa na Izala a jihar Kano.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like