Duk Mai Son Jin Abinda Zan Fada Kan Shagalin Auren Ƴar Ganduje, Ya Sameni A Ofis – Malam Aminu Daurawa


“A ranar Asabar [Maris 3] na tafi Sakkwato misalin karfe 1:00 jim kadan bayan daura auren, domin halartar bitar littafin Dakta Mansur na Iziyya. Bayan kwana biyu a Sakkwato na wuce jihar Zamfara domin yin wa’azi.

“Na kwana daya a nan sannan na wuce zuwa jihar Kaduna domin halartar shirin awa biyu a gidan Talabijin na DITV. Ranar Juma’a na yi wa Mata wa’azi a Rigasa. Daga baya na jagorancin hudubar Juma’a, bayan Sallar Magariba na yi Wa’azi a masallacin Sheikh Rabi’u Daura.

Ranar Asabar da safe na yi wa Mata Wa’azi a Masallacin Sultan Bello, daga nan na dawo jihar Kano. Ga duk wadanda suke son ganina na dawo ina ofis. Kowa na son jin me zan ce akan shagalin auren ‘yar GWAMNA, yanzu ku fada min me kuke so na fada?

You may also like