Duk Wanda Ya ke Ganin Ya na da Wata Kasa Ba Nijeriya ba, a Sauka Lafiya – Shugaba Buhari


 

Shugaba Muhammadu Buhari ya fada ma ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa na iya kokarinta wajen inganta rayuwar al’umma, amma duk wanda bai gamsu ba, ya ke ganin yana da wata kasa da ta wuce Nijeriya,  toh ya tafi a dawo lafiya, amma su za su zauna su gyara kasarsu.

A wata sanarwa da ya fitar, mai baiwa shugaban shawara a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu shi ya bayyana cewa shugaban ya fadi haka a wajen ganawar da ya yi da dattijan yankin Niger Delta da aka yi a jiya.

Ganawar da aka yi da dattijan yankin na Niger Delta na da nufin tattauna hanyoyin da za’a kawo karshen rikice rikicen da tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin ci gaba da yankin ke fuskanta.

Sai dai wannan magana ba ta yi wa ‘yan Nijeriya da yawa dadi ba, yayin da wasu ke ta tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta.

Wasu ke ganin shugaban ya fara kaurin suna wajen subutar baki, wasu kuma na ganin cewa kawai tsantsar mugunta ne. Wani ya yi kira da shugaba Buhari da ya ziyarci ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke Nijeriya ya ga yadda ake barin kasar zuwa kasashen waje, inda ya kara a cikin mamaki cewa har da kasar Moldova, yayin da wani kuma ya kira gwamnatin mafi muni akan mulkin soja.

Menene ra’ayinku? Shin kuna ganin cewa wadannan maganganun ba su yi tsauri ba? Shin akwai laifi ga maganar ta shugaba Buhari?

 

 

You may also like