Duk wanda ya kwarmata masu ɓoye sabbin kuɗaɗe zai samu tukuici – EFCC



Abdurrasheed Bawa

Asalin hoton, efcc

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce bankunan kasuwanci ne suka janyo tarnaƙi wajen ganin sabbin kuɗi sun wadata a hannun jama’a.

EFCC ta ce bayanai daga Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa zuwa yanzu, CBN ya buga sabbin takardun kuɗi sama da naira biliyan 400, amma bankuna sun ƙi fitarwa su bai wa jama’ar ƙasar.

Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa a wata tattaunawa da BBC, ya buƙaci ‘yan Najeriya su tona asirin masu ɓoye sabbin kuɗi, don ganin hukumar ta je ta ƙwace su.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like