
Asalin hoton, @GOVERNORINUWA
A Najeriya, yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan wa’adin da babban bankin ƙasar ya bayar na daina amfani da tsofaffin kuɗi, gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya ce dukkanin takwarorinsa na goyon bayan ƙarar da aka shigar na soke wa’adin.
Gwamnonin, waɗanda suka hada da na jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Kogi sun buƙaci kotun kolin ta taka wa babban bankin burki game da wa’adin.
A tattaunawarsa da BBC, gwamnan jihar Gomben, ya ce tsarin da CBN ɗin ya kawo ba zai yi wa al’ummar arewacin ƙasar daɗi ba ganin cewa bankuna ba su wadata yanda komai zai tafi daidai ba.
Ya ce ba a faɗa wa shugaban ƙasa gaskiya ba kan abubuwan da ke faruwa na harkokin banki a arewa sannan kuma ba su buga isassun takardun kuɗi da za su wadaci al’umma ba.
”Ya kamata in ka kawo kuɗinka koda dubu biyar ne a canza maka su a take, in kuma ba haka ba, buƙatar da muka ce shi ne a bar waɗannan takardun kuɗin kala biyu su tafi har zuwa wani lokacin da babban bankin zai iya tanadar isassun takardun kuɗi,” in ji gwamnan.
Ya ce abin da ya sa suka kalubalanci wannan tsari ba wani abu ba ne illa su ne suke kusa da al’umma kuma suka san matsalar da suke ciki ba wai domin buƙatar kansu ba.
Gwamnan ya ce tun shekarar da aka kawo tsarin cewa duk wani banki na kasuwanci sai yana da jari na biliyan 25, daga lokacin ne arewacin ƙasar ya fita daga tsari na bankuna na Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewa akasarin masu iko da bankunan ƙasar sun fito ne daga kudancin ƙasar.
Ya ce babu network a yawancin ƙauyuka da mutane za su iya amfani da shi wajen tura kuɗi sannan mutane ba su da ilimin yanda ake tura kuɗaɗe, wanda ya ce hakan zai sanya masu rayuwa a irin waɗannan wurare su gaza buɗe asusun ajiya a banki.