Wani dan sama jannati dan kasar Japan Norishige Kanai ya kara tsayin santimita 9 bayan ya zauna na tsawon makwanni 3 a duniya wata.
A wani sako da ya fitar ta shafinsa na Twitter Kanai ya ce, yana da labari mai dadi ga jama’a. Bayan ya ce duniyar wata ya yi makwanni 3 sai ya auna tsayinsa inda ya ga ya karu da santimita 9 sai kace wata bishiya da aka shuka.
Ya ce, a lokacin da ya ke dawo wa duniya a watan Yuni da kumbon Soyuz ya yi fargabar ko kujerar ciki ba za ta dauke shi ba.