Easter: Yesu zai iya dawowa a kowane lokaci daga yanzu – Rabaran Mati...

Asalin hoton, Getty Images

A yau ne mabiya addinin kirista a kasashen duniya ke gudanar da bikin Easter Monday, don tunawa da tashin Yesu Kiristi daga matattu, kamar yadda mabiya addinin suka yi imani.

Kiristocin na gudanar da bukukuwan ne bayan kammala addu’o’i tare da juyayin tunawa da ranar da aka bayyana cewa Romawa sun gicciye Yesu a juma’ar da ta gabata.

Rabaran Murtala Mati Dangora shi ne limamin cocin Ecwa da ke jihar Kano, a tattaunawarsa da BBC ya ce Easter Monday ranar murna ce da ya kamata kowane Kirista ya martaba.

Ya ce tashin da Yesu Almasihu ya yi daga matattu wani tabbaci ne da ke nuna cewa akwai ranar da duk wani ɗan adam da ya mutu zai tashi.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like