Gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa wajen sa ido kan bakin da ke shigowa Nijeriya bayan rahoton barkewar annobar cutar Ebola a Jamhuriyyar Congo.
Rahotanni daga Jamhuriyyar Congo sun tabbatar da cewa a halin yanzu kimanin mutane 17 ne suka mutu sakamakon cutar. Idan ba a manta ba, a shekarun baya da cutar ta barke kasar Laberiya, wani dan asalin kasar ya shigo Nijeriya inda ya yada cutar wadda ta yi sanadin mutuwar wasu ‘yan Nijeriya.