Ebonyi Za Ta Gyara Halayen Tsoffin Yan Kungiyar IPOB Gwamnatin jihar Ebonyi ta kammala duk wani shiri na tsugunar da ‘yan asalin jihar wadanda aka yaudara wajen shiga kungiyar nan ta IPOB.

Ya ci gaba da cewa an yi amfani da yanayin rashin aiki da ke tsakanin matasan wajen jan hankularsu kan shiga kungiyar inda ya ce gwamnonin Kudu maso Gabas sun tanadi wani tallafi ga wadanda suka fice daga kungiyar.

A cewarsa, gwamnonin yankin sun dauki matakin haramta kungiyar ta IPOB ne saboda tana neman Jefa rayuwar al’ummar Igbo milyan 12 da ke fadin kasar nan cikin mummunar hadari inda ya nuna cewa ba su nadamar haramta kungiyar ba.

You may also like