Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta zabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin babban mai shiga tsakani don magance takaddamar siyasar da ta kunno kai a kasar Gambiya bayan kin amincewar da sakamakon zaben shugaban kasar da shugaba Yahya Jammeh yayi.
A wata sanarwar da aka fitar a karshen taron Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka gudanar jiya a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya, shugabannin sun amince da nadin shugaba Buhari a matsayin babban mai shiga tsakanin da kuma shugaban kasar Ghana mai barin gado John Dramani Mahama a matsayin mai taimaka masa a kokarin da ake yi na magance rikicin da ke kokarin kunno kai a kasar Gambiya.
A jiya Asabar ne dai shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS suka gudanar da wani taronsu na musamman don tattauna matsalar kasar Gambiyan da kuma yadda za a bullo wa lamarin inda suka kirayi shugaba Yahya Jammeh da ya mika mulki ga zababben shugaban kasar Adama Barrow a karshen wa’adin mulkinsa da zai kare a ranar 18 ga watan Janairun nan.
Shugabannin kungiyar dai sun ce ba su kore yiyuwar amfani da duk wata hanya wajen tilasta wa shugaba Jammeh ya sauka daga karagar mulkin ba, ciki kuwa har da yiyuwar amfani da karfin soji wajen tilasta masa.
A makon da ya gabata ne wasu shuwagabannin kasashen yankin da suka hada da shugabannin Liberia, Nijeriya,Ghana da Saliyo suka tafi kasar Gambiya don shawo kan shugaban Jammeh ya amince da sakamakon zaben amma ba tare da samun nasara ba.