ECOWAS Za Ta Ci Gaba Da Kokarin Magance Rikicin Gambiya Cikin Ruwan Sanyi


4bkc3f18be763ajt07_800c450

Shugabar kasar Liberiya kana kuma shugabar kungiyar ECOWAS ta tattakin arzikin kasashen yammacin Afirka, Ellen Johnson Sirleaf ta sanar da cewar shugabannin kungiyar za su ci gaba da aikin da suke yi na shiga tsakani da nufin kawo karshen rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Gambiya cikin ruwan sanyi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugabar Liberiyan, Ellen Johnson Sirleaf, ta sanar da hakan a wata ganawa da ta yi da manema labarai bayan ganawar da shugabannin yankin suka gudanar a kasar Ghana wajen rantsar da sabon shugaban kasar da aka yi a jiya Asabar inda ta ce har ya zuwa yanzu dai shugabannin kungiyar ta ECOWAS suna fatan ganin an magance rikicin Gambiyan cikin ruwan sanyi.

Haka nan kuma yayin da aka tambaye ta dangane da batun amfani da karfin soja wajen kawar da shugaba Yahya Jammeh daga karagar mulki kuwa, shugabar ta Liberiya ta ce: A’a, har yanzu dai suna ci gaba da bin tafarkin ruwan sanyi, kamar yadda kuma ta ce suna ci gaba da sanya ido kan hukuncin da Kotun koli ta kasar za ta yanke dangane da karar da shugaba Jammeh ya shigar inda ya ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar.

Ministan harkoki wajen Nigeriya Geoffrey Onyeama ya sanar da cewa a gobe Litinin, shugabannin kungiyar ECOWAS din za su gudanar da wani taro a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan don tattauna matakan da ya kamata a dauka nan gaba, saboda wasu labarai masu tada da hankali da ya ce shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS din kan rikicin Gambiyan ya samu kan rikicin, sai dai bai yi karin bayani ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like