Kungiyar Raya Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ( ECOWAS) za ta rage yawan dakarun sojin ta data tura a Gambia saboda a cewar ta kasar ba ta fuskantar matsalar tsaro.
Wannan dai na zuwa ne bayan da sabon shugaban kasar Adama Barrow ya koma Banjul fadar mulkin kasar a jiya Juma’a, bayan da tsohon shugaba Yahya Jammeh ya bar kasar bayan matsin lamaba ta fuskar diplomatsiya da kuma barazanar daukan matakin soji da ECOWAS ta yi masa.
Kanfanin dilancin labaren AFP ya rawaito kwamnadan rundunar ta ECOWAS, Janar Francois Ndiaye, ya shaida hakan a cikin wata sanarwa inda ya ce yanayi ya inganta, don haka aka yanke wannan shawara.
Wannan matakin kuma a cewar sa ya shafi sojojin kasa sai kuma na rundinar sojin sama da kuma na ruwa wadanda za’a rage yawansu sannu a hankali.
Ba’a dai bayyana yawan sojojin ECOWAS da ke cikin kasar ta Gambia ba, amma a baya an shirya tura dakaru 7,000 daga kasashe biyar, ciki har da Senegal, da Najeriya, da Ghana.