Edward Snowden ya zama dan kasar Rasha | Labarai | DWShugaban Rasha Vladimir Putin ya bai wa tsohon dan Amirka kuma dan kwantaragi kan harkoki Edward Snowden takardar zama dan kasa bisa wata doka da shugaban na Rasha ya rattaba wa hannu a wannan Litinin.

Snowden na daya daga cikin mutane 75 ‘yan kasashen waje da dokar ta zayyana an basu shaidar zama ‘yan kasar Rasha. An wallafa dokar a shafin Internet na gwamnati.

Snowden wanda tsohon dan kwantaragi ne a hukumar tsaron kasa ta Amirka ya dade yana zaune a Rasha tun shekarar 2013 domin kauce wa hukunci a Amirka bayan da ya kwarmata wasu bayanan sirri inda ya bankado shirin gwamnatin Amirka na leken asiri.
 You may also like