EFCC na Binciken Surukin Buhari


 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC za ta fara binciken sabon surukin shugaba Buhari
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da fara wannan binciken na Gimba Kumo wanda tsohon shugaban bankin ba da lamunin mallaka ko gina gidaje ne “FEDERAL MORTGAGE BANK”
Tuhumar ta kunshi binciken Gimban da karkatar da kudi da su ka ba shi damar gina wani babban otal a Gombe da ke arewa maso gabashin kasar nan.
Otal din mai suna MAIDUGU na Unguwar mafiya hannu da shuni a garin Gombe GRA kuma yana daga masaukan baki mafi tsada.
A makon jiya ne a ka daura auren Gimba da ‘yar shugaba Buhari Fatima a Daura da ke jihar Katsina.
Wannan bincike na nuna ba sani ba sabo kan yaki da cin hanci na gwamnatin canji ta Buhari.

You may also like