EFCC Na Da Ikon Cafke Duk Wani Mai Laifi – Osinbajo


Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbanjo ya jaddada cewa doka ta ba EFCC cikakken ikon cafke duk wanda ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa.

Ya ce Shugaba Buhari bai katsalanda cikin harkokin hukumar EFCC ballantana ya bayar da umarnin a cafke wani abokin adawar siyasarsa inda ya ce a maimakon haka ma, Buhari ya ba EFCC karfin guiwar gudanar da ayyukanta a bisa tsarin dokar da ya kafa hukumar.

You may also like