EFCC sun kama tsohon kwamissiona kan sace kudi Naira Millian 83


l

Hukumar Yaki da cin hanci da rasahwa  EFCC ta kama tsohon kwamissionan mai kula da kayan gwanati na jihar Ebonyi, Engineer Benjamin Ogbonnaya Okah, da zargin karban tukwici har naira millian tamanin da uku N83million.

An kama shi ne takarda me dauke da hatimin jihar Ebonyi na kwantiradin wani kamfanin hadin gwiwan na America. Califco da aka tsayar da ikin tun 2012,duk da cewa gwanatin ta biya kudin fara kwangilan dallar Amurka $8.2Million a cikin asusun kamfanin.

Bincike yanuna cewa  adressin  da kamfani  suka miki jihar Abuja da Ebonyin duk karya ne,don bincike ya nuna cewa kwamissionan ya karbi tukwici daga kamfanin na N83 million tsakanin talatin ga watan juli,2012 da talatin ga watan desamba,2014 ta hanyar kamfanoninsa: Global Victory Allied Company and Mahco Mega Nigeria Limited.

 

You may also like