Hukumar EFCC ta bankado wasu rukunin gidaje mallakar Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Misis Diezani Alison-Maduekwe wanda ke kan titin Diepreye Alamieyeseigha Street a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.
Ana dai hasashen EFCC za ta tuhumi wasu shugabannin bankuna biyar wadanda suka taimakawa Tsohuwar Ministar wajen cire dala milyan 153 daga asusun kamfanin mai na Kasa wato, NNPC a shekarar 2014.
Haka nan kuma, a halin yanzu, Shugaban EFCC, Ibrahim. Magu ya isa birnin Londam na kasar Birtaniya don ci gaba da bincike game da kudade da kuma kadarorin da Misis Diezani ta boye a kasar.