Hukumar EFCC ta cafke dan takarar kujerar Gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Alhaji Bala Bello Tinka bisa zarginsa da hannun wajen almundahanar wasu makudan kudade na zaben 2015.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na biyu da EFCC ke gayyatar Bello Tinka bisa zargin karkatar da wadannan kudade kuma yana daga cikin makusantan Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Dankwambo. Tuni dai, EFCC ta tabbatar da kammala maka dan takarar Gwamnan kotu.