A jiya Litinin ne hukumar EFCC ta cika hannu da tsohon ministan Abuja Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi), kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ra rawaito.
Saidai majiyar tamu ba ta tabbatar da dalilin kamun nasa ba, amma har zuwa yanzu Kauran Bauchin wanda ya rike mukamin ministan Abuja daga 2010 zuwa 2015 yana tsare a hedikatar hukumar dake Abuja.
Yanzu haka dai tsoffin takwarorin Sanata Bala Mohammed da suke tsare tare da shi a komar ta EFCC, sun hada da tsohon karamin ministan tsaro Musiliu Obanikoro, tsohon ministan sufuri, Femi Fani-Kayode da kuma kakakin tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin Jonathan, wato Reuben Abati.