EFCC Ta Fara Binciken Wasu Manyan Jami’an Gwamnatin NejaHukumar EFCC ta fara Bincken wasu manyan jami’an gwamnatin Jihar Neja inda ta gayyaci Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnatin jihar, Mikail Alamin Shekwoaga, da kuma Shugaban Hukumar ci gaban kiwon lafiya ta jihar, Dakta Yahaya Na’uzo.

A cikin takardar gayyatar da hukumar EFCC ta gabatarwa ofishin Sakataren gwamnatin ta nuna cewa ana zargin shugaban ma’aikatan Fadar gwamnatin da yin rub da ciki da wasu makudan kudade kamar yadda shi ma, Dakta Yahaya ya yi almundahanar wasu kudade a hukumar tasa.

You may also like