EFCC Ta Fara Bincken Modu Sheriif Kan Zargin Rashawa


Hukumar EFCC ta gayyaci Tsohon Gwamnan Borno, Alhaji Modu Sheriff inda ta yi masa tambayoyi kan wasu makudan kudade da ake zargin ya karkatar a lokacin da yake Gwamna.

Rahotanni sun nuna cewa Modu Sheriff ya isa hedkwatar EFCC ne da misalin Karfe goma sha daya na safen jiya Litinin kuma hukumar ta bayar da belinsa tare da ci gaba da gudanar da bincke a kansa.

You may also like