Hukumar hana tu’annati da satar kudaden gwamnati ta jihar Kano, wato Kano State Public Complaint And Anti-Corruption Commission, ta bankado wata babbar badakala wadda ta shafi tsohuwar Kwamishiniyar jihar da ta ajiye aikinta a watan Fabrairu.
An gano wasu kudade ne da suka kai N100m na kananan hukumomi, wadanda aka kwashe daga asusun bai daya na kananan hukumomi, aka kuma mika su ga wani asusun tun a 2016 domin su haihu. Wannan dai babban laifi ne da ya shafi kananan hukumomi da sauran dokoki da suka shafi bankuna da hada-hadar kudi da ma aikin gwamnati.
Ashe wannan binciken da ma wasu dalilai na daga cikin dalilan da ya sanya Hajiya Aisha Mohammed Bello kwamishiniyar kudi ajiye aikinta.
Binciken ya nuna, ta hada kai ne da Managing Director ta Grassroots Micro Finance Bank, Hajiya Farida M. Tahir inda aka ajiye kudin, watakil kuma boyo ne, ko dai don riba, ko kuma don lamushe su in an manta dasu.
Za dai a cigaba da fadada bincike don gano sauran wadanda suke da hannu wajen boye wannan kudaden.