Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC, a ranar Talata ta gurfanar da tsohon ministan albarkatun ruwa,Alhaji Muktari Shagari tare da wasu mutane hudu a gaban mai shari’a, Idrissa Kolo na babbar kotun tarayya dake Sokoto.
Ana tuhumarsu da aikata laifuka biyar ciki har da hada baki wajen aikata almuundahanar kudade da yawansu ya kai miliyan ₦500,000,000.
Sauran mutane hudu da aka gurfanar da su tare da ministan sun hada da Abdullahi Wali, Nasiru Bafarawa, Ibrahim Gidado da kuma Ibrahim Milgoma.
Hukumar na tuhumarsu da karbar kudin daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Diezani Allison Madueke, gabanin zaben shekarar 2015.
Dukkanin mutanen sun musalta zargin da ake musu.