EFCC ta kama mutum sama da 65 kan zargin sayen kuri’u



EFCC

Asalin hoton, OfficialEFCC/Twitter

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa arzikin Najeriya ta’annati ta ce ta kama kimanin mutum 65 da suka aikata laifukan sayen kuri’a yayin zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris a jihohi 28.

Hukumar ta ce jami’anta a shiyyar Ilorin sun kama mutum ashirin wadanda ake zargi, yayin da wasu 13 kuma aka kama su a jihar Kaduna.

Tawagar hukumar da ke sa ido kan zaben a Port Harcourt sun kama kimanin mutum 12 bisa samun su da aikata laifukan da suka shafi bai wa masu zabe kudi domin jan ra’ayinsu ga dan takarar da suke goyon baya, yayin da kuma aka cafke mutum hudu a Calabar ta jihar Kuros River. Sauran wadanda ake zargi an kama su ne a jihohin Gombe da Sokoto da Kebbi da kuma Neja.

Wadanda aka kama a Kaduna sun hada da maza 10 da mata uku a cewar EFCC. Jami’an hukumar dake tattara bayanan sirri ne suka kama su a lokacin da suke kan aikin sa ido a zaben.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like