EFCC ta kama tsohon sakataren gwamnatin tarayya Pious Anyim


Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta tabbatar da kama tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim.

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun ya fadawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ranar Juma’a cewa an kama Anyim ne kan wani bincike da hukumar keyi.

NAN ya rawaito cewa Uwujaren bai bada cikakken bayani ba kan dalilin da yasa hukumar ke tsare da Anyim.

Anyim ya kasance shugaban majalisar dattijai tsakanin shekarar 2000 zuwa 2003.

Ya kuma kasance sakataren gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like