EFCC ta kama wasu yan damfara 10 a Legas


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta kai samame wani gidan rawa dake Lagos inda ta kama mutane 12.

Ana zargin mutanen da aka kama da laifin aikata zamba ta hanyar yin amfani da na’ura mai kwakwalwa.

An kama mutanen ne bayan da hukumar yaki da cin hancin ta kai samame wani gidan rawa da ake kira ‘Club 57’ dake yankin Ikoyi a jihar ta Lagos.

Hukumar tace wasu daga cikin mutanen da ake zargi sun gudu sun bar motocinsu masu tsada, inda aka bayyana cewa motoci 10 aka gudu aka bari a wurin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like