EFCC ta kame masu karkatar da kayan agaji


 

 

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta yi shailar cafke mutane 25 da ake zargi da karkatar da kayan agajin yankin Arewa maso gabashi da ke fama da rikici.

Karte Nigeria Yobe Damaturu Deutsch/Englisch

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa wato EFCC ta samu cafko mutanen farko da take zargi da karkatar da kayan agaji da aka basu don su kai wa mutanen da suka rasa muhallansu a yankin Arewa maso gabashin kasar da ke fama da rikicin Boko Haram.

Hukumar tace wani dan kasuwa da mutanensa ne take zargi da karkatar da tiriloli 65 daga cikin 333 na kayan agajin da aka basu dakonsu. Ya zuwa yanzu dai hukumar ta samu cafke mutane 25 da ke da hannun a wannan laifi.

Malam Umar Abba Muhammad shi ne mataimakin daraktan gudanarwa na hukumar ta EFCC ya yi bayanin yadda suka kai ga kame mutanen, inda ya ce bayan bincike ne suka kama masu laifi. Nan bada dadewa ba ne za a gabatar da su a kotu.

You may also like