Hukumar EFCC ta mika bukatar kwato wasu manyan gidajen Alfarma mallakar Tsohuwar Ministar Mai, Diezani Alison- Maduekwe wanda ta gano kwanan nan a Daular Tarayya Larabawa wato, Dubai.
Wata majiya daga hukumar ta nuna cewa a kiyasta kudaden gidajen guda biyu a kan Naira Bilyan 7.1 kuma idan hukumar ta samu nasarar kwato gidajen, zai kasance yawan kudade da kadarori da aka kwato daga hannun Tsohuwar Ministar ya kai Naira Bilyan 70.