EFCC ta nemi kotu ta janye belin da ta bawa Olisa Metuh


Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta EFCC ta nemi babbar kotun tarayya dake Abuja kan ta janye belin da ta bawa Olisah Metuh tsohon mai magana da yawun jam’iyar PDP.

Metuh na fuskantar shari’a kan zargin sa da ake yi na yin amfani da wani kamfaninsa mai suna  Destra Investment Limited wajen karbar miliyan ₦400 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Sambo Dasuki a shekarar 2014.

An daga shari’ar ranar Litinin 22 ga watan Janairu bayan da aka ce an kwantar dashi a Asibitin Koyarwa na Nnamdi Azikiwe dake Nnewi jihar Anambra.

Ya yin zaman sauraron shari’ar na ranar Talata, hukumar ta EFCC ta nemi kotun kan ta janye belin da ta bawa Metuh ta kuma tura shi gidan yari domin haka ya bashi damar y halartar zaman shari’ar tasa.

Sylvanus Tahir lauyan hukumar EFCC da yake mai da martani kan neman kotun ta daga ranar a da lauyoyin Metuh suka yi saboda rashin lafiyarsa, ya zargi lauyoyin masu kariya da kawo tarnaki ga shari’ar.
 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like