EFCC ta saki Babachir Lawal 


Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta EFCC ta saki Babachir David Lawal tsohon sakataren gwamnatin tarayya.

Lawal wanda ke tsare a ofishin EFCC tun ranar Laraba an bayar da belinsa da yammacin yau  Juma’a.

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari, ya sallame shi daga aiki bayan da wani kwamitin da ya kafa ƙarƙashin jagoranci mataimakin shugaban ƙasa Osinbajo ya same shi da laifin almundahana.

An zargeshi da yin amfani da kamfaninsa mai suna Rolavision Engineering Limited wajen karkatar da wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai miliyan ₦200 ta hanyar bawa kamfanin kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe.

Wannan cigaban da aka samu na zuwa ne sa’o’i 24 bayan wasikar da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba Buhari inda a ciki yake zarginsa da boye mutanen dake jikinsa daga tuhuma kan aikata cin hanci da rashawa.
Sai dai hukumar  EFCC ta musalta haka inda tace kama tsohon sakataren da tayi bashi da alaƙa da wasikar tsohon shugaban ƙasar.

You may also like