EFCC ta saki Jamilah Tangaza


 

2015_10_19_48032

 

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, ta saki shugabar sashin kula da mallakar filaye a hukumar mulki ta birnin Abuja, Hajiya Jamilah Tangaza.

Makonni biyu da suka gabata ne dai hukumar ta EFCC ta kama Misis Tangaza, wadda tsohuwar shugabar sashen Hausa na BBC ce, bisa zargin karkatar da kudade da yin kwangila ba bisa ka’ida ba.

Amma ta yi fatali da wadannan zarge-zargen.

Wata majiya da ke da kusanci da ita ta shaida wa BBC cewa da yammacin ranar Talata ne ta isa gidanta bayan barin ofishin hukumar.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya shaida wa BBC cewa an bayar da belinta bayan da suka ga cewa bai kamata a ci gaba da tsare ta ba ba tare an tuhumeta a gaban kotu ba.

Sai dai ya musanta cewa suna yi mata bita-da-kulli ne kawai domain sun kasa samunta da laifi, yana mai cewa za su ci gaba da gudanar da bincike.

Hakazalika ya ki yin karin haske kan sharudan belin nata.

Tunda farko wasu gungun lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama a Abuja, sun yi barazanar kai hukumar kotu bisa zargin cewa tana take mata hakkin ta saboda tsareta ba tare da yi mata shari’a ba.

Ita dai EFCC ta zargi Jamilah Tangaza ne da amfani da kamfaninta wurin yin kwangila a lokacin da take baiwa tsohon ministan Abuja, Bala Muhammed, shawara kan harkokin watsa labarai.

Sannan ta zarge ta da aikata ba daidai ba a ma’aikatar tantance filaye ta birnin na Abuja inda take aiki a yanzu.

Sai dai ta yi watsi da dukkan wadannan zarge-zargen.

You may also like