EFCC Ta Shiga Binciken Alkalan Nijeriya Guda 8


 

 

Akalla alkalan Nijeriya guda 8 da ma’aikatan kotu guda biyu ne ke fuskantar bincike a sakamakon zargin cin hanci da rashawa da ake yi musu.

Wannan batu ya bayyana ne a wata sanarwa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fitar a jiya Alhamis inda ta fadi cewa za ta gurfanar da alkalan da ta samu da laifi a gaban kuliya.

Sai dai ba ta bayyana sunayen wadanda ta ke binciken ba, amma dai ana kyautata zaton cewa wadanda hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS ta kaiwa Sumame na ‘yan kwanakin da suka gabata.

Kwanaki 6 kacal da suka gabata ne jami’an hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS suka kaiwa alkalan sumame, inda suka yi awan gaba da su a bisa zargin cin hanci da rashawa, jami’an sun kuma ce sun samu makudan kudade a gidan alkalan. Daga bisani an bayarda belinsu yayin da aka shiga binciken na su ka’in da na’in.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren ya bayyana cewa wasu daga cikin alkalan sun bayarda hadin kai wajen bayyanawa hukumar wasu batutuwa masu muhimmanci da zai yi mata amfani a binciken da ta ke yi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like