EFCC ta tsare Shekarau da Wali


Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau da kuma tsohon ministan harkokin waje Ambasada Aminu Bashir Wali kan kudin da ake zargin sun karba na yakin neman zaben shugaban kasa Gudluck Jonathan a shekarar 2015.

Ana zargin jam’iyar PDP a jihar Kano da karbar kudin da yawansu ya kai miliyan ₦950.

A cikin watan Mayun shekarar 2016 hukumar ta yiwa mutanen biyu tambayoyi bisa zargin cewa sun karbi miliyan ₦25 daga cikin kudin.

An raba kudaden ne a tsakanin manyan yayan jam’iyar PDP na jihar domin yaƙin neman zaben tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan.

Manyan yan siyasar sun ziyarci ofishin na EFCC tare da dumbum magoya bayansu.

Wata majiya dake hukumar ta ce akwai yiwuwar gobe Alhamis za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu.

You may also like