EFCC ta tsare tsohon gwamnan Kaduna Ramadan Yero


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Taannati EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna,Moukhtar Ramalan Yero, tsohon karamin ministan ma’aikatar wutar lantarki, Nuhu Somo Wya, da kuma wasu mutane biyu.

Jami’an EFCC dake ofishin hukumar na shiya dake Kaduna su ne ke tsare da mutanen kan kudin yakin neman zaben shugaban kasa miliyan ₦700 da jam’iyar PDP ta bayar gabanin zaben shekarar 2015.

Sauran wadanda ake tsare da su sun hada da Abubakar Gaya Haruna, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, da kuma Ishaq Hamza, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna lokacin mulkin Ramalan Yero.

Mutanen da suke tsare sun shafe watanni biyu suna ziyartar ofishin hukumar kamar yadda tsarin bincike na hukumar ya tanada.

Jaridar The Cable ta gano cewa hukumar ta tsare su ne a ranar Laraba domin ta gurfanar da su gaban kotu ranar Alhamis.

“Za a saurari shari’ar gobe, saboda haka zan iya tabbatar maka da cewa tsohon gwamnan yana nan tare damu kuma za a gurfanar da su gaban kotu a gobe tare da sauran mutanen uku,”a cewar wata majiya dake hukumar.

You may also like