EFCC Za Ta Gabatar Da Shaida Kan Yadda Nyako Yayi Babakere Da Biliyan 29Hukumar EFCC  za ta gabatar wa kotu shaidu kan yadda tsohon Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako ya yi amfani da asusun ajiyar banki har 30 wajen wawure Naira Bilyan 29 na kudaden jihar.
Haka ma, EFCC ta bayyana cewa Nyako ya yi amfani da wasu kamfanoni wajen satar kudaden jihar. Sai dai lauyan da ke kare tsohon Gwamnan, barista Kanu Agabi ya nuna rashin gamsuwa da sahihanci shaidun da EFCC ta gabatar inda ya nemi kotu ta ba shi damar tantance bayanai kafin a gabatar da su a matsayin shaid.

You may also like