EFCC Zata Sa Idi Kan Yadda Gwamnoni Za Su Sarrafa Tallafin Gwamnatin Tarayya



Shugaba Buhari ya ba hukumar EFCC umarnin sa Ido kan yadda gwamnoni za su sarrafa kudaden tallafi na Naira Bilyan 522.72 da gwamnatin tarayya ta ba su bayan da shugaban ya nemi gwamnonin su yi amfani da wani bangare na kudaden wajen biyan basussukan albashin ma’aikatansu.
Tun da farko dai gwamnonin sun cimma yarjejeniya da Ministan kudi kan kada a bayyana adadin kudaden da kowace jiha ta samu don kada al’ummomin jihohinsu su kara matsa masu lamba kan wasu bukatu na daban. Sai dai ana hasashen kowace jiha za ta iya samun Naira Bilyan 14.5.

You may also like