El-Rufa’i Da Nuhu Ribadu Sunci Amanata – Atiku Abubakar 


Atiku Makaryaci Ne, Son Ya Shugabanci Nijeriya Ne Ya Sa Yake Neman Wanke Kansa Kan Tabargazan Da Ya Tabka A Baya. Sannan Kuma Yana Da Hannu A Rikicin Dake Bulluwa Tsakanin ‘Yan Majalisu Da Buhari, Inji EL-RUFAI
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zayyana yadda gwamnan Kaduna na yanzu Malam Nasir El-Rufai da tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu suka ci amanarsa a lokacin da suka samu sabani da shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Atiku ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da mujallar Zero Tolerance, inda ya fadi wasu daga cikin dalilan da yake ganin ya sa El-Rufai ya yi masa kazafi akan wasu abubuwan da bai faru ba.
Atiku ya ce daya daga cikin dalilan shine kin marawa kara wa’adin mulki da kums sharin da aka yi masa wai wasu sun nemi kudi a hannunsa domin tabbatar da nadin El-Rufai Ministan Abuja a wancan lokacin.
Ya ce kin hakan ne ya sa El-Rufai da Nuhu suka tattaro ire-iren wadannan abubuwa domin ganin an wulakanta shi. Amma duk da haka kotu ta wanke shi.
“Shi kuma Nuhu Ribadu ko da ya zo yana rokon in yafe masa laifin da ya yi mini na ce masa ya tafi gidan talabijin inda ya fadi cewa wai ni barawo ne ya fada cewa karya yake yi ba haka bane.

“Nan dai ya yi ta rokona har na ce masa na hakura.
“Maganar neman gwamnansa kuma na aika a gaya masa tun a wancan lokacin kada ya canza sheka yaki ji.
A gefe daya kuma, a martanin da gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai kara rura wutar rikicin ya yi, inda ya ce maganar hannun jari a kamfanin Transcorp da Atiku ya ce ya yi masa tayi ba shi da wata masaniya akan wai ya karba har ya ba Atiku daga ciki..
“Maganan kudi kuma da na ce wai wasu sanatoci sun bukace ni da in basu kafin su amince na zama minista, abinda Atiku ya yi yanzu ya tabbatar da hakan ne.
” Duk da cewa Atiku ya fara kamfen din neman zama shugaban kasa a 2019, ya na neman wadanda zai dora wa laifi ne kawai, irin mu domin ya wanke kansa.

El-Rufai ya kara da cewa ko abubuwan da yake faruwa a majalisa tsakanin shugabannin majalisa da Shugaban kasa Buhari yana da nasaba da wani shiri na Atiku. Sannan ya ce maganar hannu da yake da shi a wata badakalar kudi a kasar Amurka na nan, idan kuma ba haka ba ya fito yayi bayani akai.

You may also like