Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Sanata Suleman Hunkuyi ya koka kan cewa Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i na shirin sake rusa masa gida da ke cikin garin Kaduna.
Dan majalisar ya nuna cewa hukumar kula da filaye ta jihar ta bashi wa’adin kwanaki 30 kan biya harajin kasa na Naira milyan 30 ko kuma a rusa masa gidansa da ke titin Inuwa Wada. A shekaranjiya Talata ne dai, El Rufa’i ya rusa gidan dan majalisar wanda bangaren jam’iyyar APC na jihar ke amfani da shi a matsayin ofishinta.